Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya tabbatar da cewa jami’an tsaro sun gano maboyar ’yan bindigar da suka sace ɗalibai mata 25 daga makarantar kwana ta Maga, dake Jihar Kebbi.
Da yake jawabi a Birnin Kebbi, Matawalle ya ce an ƙara tsaurara bincike da leƙen asiri, tare da tsara matakan ceto ɗaliban ba tare da cutar da su ba. Ya ce gwamnati tana aiki sannu a hankali cikin ƙwarin gwiwa domin tabbatar da an dawo da su cikin aminci.
Ministan ya yi kira ga al’umma su ci gaba da ba jami’an tsaro goyon baya da bayanan sirri, yana mai jaddada cewa haɗin kan jama’a shi ne ginshiƙin nasarar wannan aiki.
A makon da ya gabata ne ’yan bindiga suka kai hari makarantar ta Maga suka tafi da ɗalibai mata 25, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma.
Biyo bayan haka, Shugaba Bola Tinubu ya umurci Matawalle da ya koma Kebbi domin kula da dukkan matakan tsaro da ake ɗauka. A cewar fadar shugaban ƙasa, za a yi amfani da ƙwarewar da Matawalle ya samu a yaƙi da masu garkuwa da mutane lokacin da yake gwamnan Zamfara.


