Gwamnatin Neja ta dakatar da harkokin karatu a jihar

0
7

Gwamna Umaru Bago na jihar Neja, ya sanar da rufe dukkan makarantun jihar, bayan sace wasu daliban makarantar St. Mary da ke garin Papiri na karamar hukumar Agwara.

Da yake jawabi ga manema labarai a Minna, Gwamnan ya ce lamarin ya girgiza al’ummar jihar, yana mai bayyana shi a matsayin abin bakin ciki da dole gwamnati ta yi gaggawar daukar mataki a kan sa.

Rufe makarantun ya biyo bayan matakin da jihohin Filato da Katsina suka dauka a baya-bayan nan, inda su ma suka dakatar da harkokin karatu saboda tsaro.

Gwamna Bago ya tabbatar da cewa gwamnati na aiki tukuru don ceto daliban tare da dawo da su cikin aminci, yana mai nanata kudirin gwamnatin jihar na daukar matakan kariya ga makarantu a duk fadin Neja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here