Adadin ɗaliban da aka sace a makarantar St Mary’s ya kai 303 — CAN

0
11

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Neja, ta bayyana cewa adadin ɗaliban da aka sace daga makarantar St Mary’s Catholic da ke Papiri, ƙaramar hukmar Agwara, ya karu zuwa 303, tare da malamai 12, wanda ya kai jimillar 315.

A ranar Juma’a ne ’yan bindiga suka kai hari makarantar, inda farkon bayanai suka nuna an sace ɗalibai 215 da malamai 12. Sai dai bayan ƙarin tantancewa da kirga daliban, an gano cewa wasu ɗalibai 88 da ake tunanin sun tsira, maimakon haka an cafke su ne yayin ƙoƙarin tserewa.

Shugaban CAN na jihar Neja, Most Rev. Bulus Yohanna, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, yana mai cewa makarantar da ƙungiyar makarantu masu zaman kansu ba su samu wata takarda ko umarnin gwamnati na rufe makarantu kafin harin ba.

Ya ce labaran cewa an yi musu gargaɗi tun farko ba su da tushe, yana mai kiran masu yaɗa jita-jita su gabatar da hujja ko su janye.

Bishop ɗin ya bayyana cewa adadin ɗaliban makarantar gaba ɗaya shi ne 629, kuma har yanzu ana ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro, shugabannin al’umma da gwamnati domin ceto waɗanda aka sace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here