Cacar baka ta ɓarke tsakanin iyayen ɗaliban da aka sace a Maga da gwamnatin Kebbi

0
15

Iyayen daliban makarantar sakandiren ’yan mata ta Maga da aka sace yaran su a jihar Kebbi sun koka cewa babu jami’in gwamnati da ya ziyar ce su domin kaje tun bayan faruwar lamarin.

Wasu daga cikin su sun shaida wa BBC cewa duk jami’an gwamnatin tarayya da aka turo zuwa Kebbi sun tsaya ne a Birnin Kebbi ko kuma a hedikwatar ƙaramar hukumar Danko/Wasagu, maimakon su isa makarantar da abin ya shafa.

Sai dai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Halliru Ali, ya karyata wannan zargi. Ya ce shi da kansa yana cikin tawagar gwamnatin jihar da ta shiga garin domin jajanta wa da duba halin da ake ciki.

A cewarsa, “Gwamna ma ya je garin da kansa,” yana mai bayyana cewa jami’an tarayya suna kai ziyarar jajanta wa ne ga gwamnatin jihar ta Kebbi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here