Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe kwalejoji 47, wanda aka fi sani da FGC, a sassan ƙasar nan saboda ƙalubalen tsaro da ake fuskanta.
Umarnin, wanda aka fitar a cikin wata sanarwa ranar Juma’a, ya nuna cewa matakin na da nufin kare rayukan ɗalibai da ma’aikata, musamman ganin yadda harin ‘yan bindiga ke ta ƙaruwa a yankuna daban-daban.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya amince da rufewar, yayin da daraktar manyan makarantun sakandare, Binta Abdulkadir, ta sanya wa takardar hannu.
An umarci dukkan shugabannin makarantun da abin ya shafa su bi umarnin nan take.
Rufe makarantun ya biyo bayan hare-hare biyu da suka faru cikin mako guda, ciki har da sace ɗalibai mata kusan 25 daga GGSS Maga a jihar Kebbi ranar 17 ga Nuwamba, inda aka kashe mataimakin shugaban makarantar. Haka kuma ranar 21 ga Nuwamba, wasu ‘yan bindiga sun kai hari makarantar St. Mary’s Catholic a Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Niger, inda har yanzu ba a bayyana adadin yaran da aka sace ba.
Ga jerin wasu daga cikin makarantun da aka rufe:
FGGC Minjibir
FTC Ganduje
FGGC Zaria
FTC Kafanchan
FGC Daura
FSC Sokoto
FGC Gusau
FGGC Gwandu
FGC Birnin Yauri
FGGC Kazaure
FGC Ilorin
FGGC Potiskum
FGC Azare
FTC Ikare Akoko
FTC Michika
…da sauran su, jimillar su 47.


