Gwamnan Kebbi ya nemi jin dalilin janye sojoji kafin sace ɗaliban jihar

0
11

Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya ce yana neman cikakken bayani daga rundunar soji kan dalilin da ya sa suka janye jami’ansu daga Makarantar GGC Maga kimanin rabin sa’a kafin ’yan bindiga su kai farmakin da ya kashe mataimakin shugaban makaranta su kuma sace dalibai 25.

Idris ya bayyana cewa gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro bayan samun bayanan sirri, kuma an tabbatar masa cewa sojoji za su kare makarantar, amma daga baya aka janye su da misalin 3:00 na dare, inda harin ya faru 3:45.

Ya ce gwamnatin jihar da ta tarayya na aiki tare domin ceto daliban, tare da gode wa Shugaban Kasa kan goyon bayan sa.

Shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa NLC, Joe Ajaero, ya ce harin magana ce ta kawar da hankali daga cigaban jihar, yana mai cewa kungiyarsu za ta tallafa wajen ƙarfafa tsaron makarantu.

A halin yanzu rundunar soji ta fara bincike kan jami’an da suka bar wurin kafin harin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here