Lauyan jagoran haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da cewa an mayar da Kanu gidan gyaran hali dake jihar Sokoto daga ofishin DSS na Abuja, bayan yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
Ejimakor ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, a yau Juma’a.
A ranar Alhamis ne alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, James Omotosho, ya samu Kanu da laifin ta’addanci tare da yanke masa hukuncin daurin rai da rai kan wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake masa.
Kotun ta kuma yanke masa hukuncin shekaru 20 da 5 kan sauran tuhume-tuhume, inda ta bayyana cewa masu shigar da ƙara sun gabatar da shaidu masu ƙarfi, yayin da Kanu bai kare kansa ba.


