Babbar Kotun tarayya ta yanke wa Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra IPOB, hukuncin daurin rai-da-rai bayan kotu ta same shi da laifin ta’addanci.
A ranar Alhamis ne Mai Shari’a James Omotosho ya sanar da hukuncin.
Kotun ta yanke masa daurin rai-da-rai kan tuhume-tuhume na 4, 5 da 6 cikin jerin tuhume bakwai da ake masa, sannan ta yanke masa hukuncin shekaru 20 a gidan yari kan tuhume ta 2.


