Tsaffin ƴan majalisar dokokin Kano sun musanta goyon bayan sanata Barau ya yi takarar gwamnan jihar

0
9
Jibrin-Barau

Tsoffin mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano daga jam’iyyar APC sun fito fili sun karyata wani rahoton da ke yawo a kafafen yada sada zumunta da ke cewa sun amince da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, a matsayin ɗan takarar gwamna na APC a zaben 2027.

Daya daga cikin tsoffin ‘yan majalisar, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana wa manema labarai cewa labarin ba gaskiya ba ne, kuma bai da wata alaka da dalilin taron da suka yi da Sanata Barau kwanan nan.

A cewarsa, Sanata Barau ne kawai ya gayyace su wajen wani taro saboda matsayin sa a jam’iyyar APC a Kano.

 Ya ce sun tattauna batutuwan da suka shafi cigaban jam’iyyar ne kawai, ba batun goyon bayan wani mai neman takara ba.

Ya kara da cewa, “Mun yi mamaki sosai ganin labarin da ake yadawa cewa mun mara wa Barau baya don ya tsaya takarar gwamna. Wannan ba gaskiya ba ne kwata-kwata.”

Tsoffin ‘yan majalisar sun ce akwai mutanen da ke kokarin tayar da kura da kawo rudani a cikin jam’iyyar APC ta hanyar yada bayanan karya. Sun jaddada cewa APC tana da tsare-tsaren ta na fitar da ‘yan takara, kuma za su goyi bayan duk wanda ya fito ta hanyar tsarin jam’iyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here