Kwamitin Raba Kuɗaɗen Ƙasar (FAAC) ya bayyana cewa an raba jimillar Naira tiriliyan 2.094 daga kudaden da suka shiga asusun gwamnatin tarayya a watan Oktoba 2025.
A cikin sanarwar da gwamnatin tarayya ta fitar, ta ce kudaden da aka tattara a watan sun kai Naira tiriliyan 2.934. Daga cikin wannan adadi, an cire Naira biliyan 115.278 a matsayin kuɗin tattara haraji, sannan aka ware Naira biliyan 724.603 domin tanadi, tallafi da wasu buƙatu na musamman.
Rabon kudaden ya ƙunshi:
Harajin cikin gida: Naira tiriliyan 1.376
Harajin ƙarin kimar kayayyaki VAT: Naira biliyan 670.303
Harajin tura kuɗi ta waya (EMTL): Naira biliyan 47.870
Daga cikin Naira tiriliyan 2.094 da aka raba:
Gwamnatin Tarayya: Naira biliyan 758.405
Jihohi: Naira biliyan 689.120
Kananan Hukumomi: Naira biliyan 505.803


