Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin a fitar da Nnamdi Kanu, shugaban kungiyyar IPOB, daga dakin shari’a saboda abin da alƙali ya bayyana a matsayin rashin ladabi da ɗabi’ar da ta saba ka’ida yayin zaman kotu.
Alƙali James Omotosho ya yanke wannan hukunci ne bayan ya yi watsi da sabbin ƙorafe-ƙorafe guda uku da Kanu ya shigar, wanda ya ce ba su da wata cancanta, musamman saboda an riga an ɗage shari’ar ne domin a yanke hukunci a wannan rana.
Alƙalin ya ce, la’akari da yadda Kanu ya nuna halayen tashin hankali da rashin natsuwa, kotun na da hurumin yanke hukunci ko da baya cikin zauren.
Tun farko, lokacin da aka fara gabatar da hukuncin da aka tsara a yau, Kanu ya yi iƙirarin cewa kotun ba za ta iya cigaba da shari’ar sa ba saboda har yanzu bai kammala mika jawabin sa na karshe ba.
Kanu, ya ɗaga murya yana zargin alƙalin da nuna son zuciya tare da cewa ba ya bin doka yadda ya dace.
Duk da haka, alƙali Omotosho ya cigaba da karanta hukuncin kamar yadda dokar kotu ta tanada.


