Yanayin rashin tsaro ya kai wani mummunan mataki a Najeriya–Kwankwaso

0
9
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Jagoran jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa tashin hankali da hare-haren da ake ta fuskanta a sassan ƙasar nan sun kai wani mataki mai tayar da hankali, wanda ke bukatar matakin gaggawa daga gwamnati da hukumomin tsaro.

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce ya zama dole gwamnati ta sauke babban nauyin da ya rataya a wuyan ta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ta hanyar ƙarfafa jami’an tsaro da ɗaukar matakan da suka dace.

Ya ce sace dalibai mata 25 a jihar Kebbi babban al’amari ne mai tada hankali, musamman ganin irin abubuwan da suka faru a baya. 

Haka kuma ya yi Allah-wadai da sacewa tare da kashe Birigadiya Janar M. Uba da ’yan ta’adda suka yi a Borno, lamarin da ya kira ɗaya daga cikin mafi muni tun lokacin da ake yaƙi da ta’addanci.

Kwankwaso ya kara da cewa ana fuskantar yawaitar sace-sacen mutane da hare-hare a jihohi irin su Zamfara da Kano, musamman a ƙananan hukumomin Shanono da Ghari, abin da ya ce na nuna koma baya a kokarin da ake yi wajen shawo kan matsalar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here