Gwamnatin jihar Kebbi ta tabbatar da cewa ɗalibai mata 24 na makarantar GGC Sakaba har yanzu suna hannun ’yan bindiga, tare da gargadin ’yan jarida su guji rawaito bayanan da ba su da tushe akan batun satar ɗaliban.
Kwamishinar Ilimin Firamare da Sakandare, ta jihar Farfesa Halima Bande, ce ta bayyana haka a Zuru ranar Talata, inda ta ce dalibai 26 ne aka sace, amma biyu, wato Salma da Hauwa’u Liman, sun tsere daga maharan da suka sace su kuma sun koma gida lafiya.
Ta ce har yanzu 24 na tsare, lamarin da ya jefa iyaye, makaranta da jihar baki ɗaya cikin tashin hankali.
“Har yanzu Ba mu san inda ake tsare da ƴan matan ba, ko irin yanayin da suke ciki.”
Ta ce jami’an tsaro na ƙoƙarin gano wa da ceto sauran ɗaliban, yayin da gwamnati ke ci gaba da tattaunawa da iyalan waɗanda abin ya shafa.
Farfesa Bande ta kuma yi gargadi kan yawaitar bayanan ƙarya a kafofin sada zumunta da wasu kafafen yaɗa labarai, wanda ta ce na iya kawo rudani da kuma kawo cikas ga aikin ceto ɗaliban.
Ta roƙi ’yan jarida su rika amfani da ingantattun bayanai, tare da kula da gaskiya da tausayi a rahoton su.
Ta tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na aiki tukuru domin ganin an ceto lafiya, tare da dawo da kwanciyar hankali a yankin.


