Hisbah ta kama ƴan daudu masu aikata masha’a a Kano

0
11

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da kama wasu daudu su 7 dake taruwa a wata mahaɗar su dake titin Zoo Road, a birnin Kano, inda ake zargin su da aikata baɗala.

Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr. Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa ƴan sun Kano daga jihohin Bauchi da Kogi, wanda suke taruwa a Zoo Road, ana ɗaukar su domin aikata fasikanci.

Hisbah, ta jaddada cewa zata saka idanu a wajen ƴan daudun ke taruwa domin tsaftace jihar Kano daga munanan halaye.

A wani cigaban jami’an rundunar Hisbah sun kama wani mutum da aka samu yana lalata da wata mace a cikin babur ɗin Adaidaita Sahu.

Mataimakin babban kwamandan, yace zasu cigaba da gudanar da bincike daga bisa ni kuma a gurfanar da wadanda ake zargin.

Daga karshe ya ja hankalin al’umma su kasance masu kiyaye dokokin Allah don samun rayuwa mai kyau a duniya da lahira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here