Ƴan bindiga sun kai wa coci hari a jihar kwara

0
9

Ƴan bindiga sun kai wa coci hari a jihar kwara

’Yan bindiga sun kai hari a cocin Christ Apostolic Church (CAC) da ke karamar hukumar Eruku, Ekiti ta Jihar Kwara da yammacin Talata, inda suka harbe malamin cocin da wani mutum sannan suka sace wasu masu ibada.

Wani faifan bidiyon harin ya nuna yadda harbe-harbe suka katse taron ibada a cocin, inda jama’a suka yi kokarin ɓuya kafin maharan su kutsa cikin cocin.

 Wasu daga cikin ’yan bindigar sun rufe fuskarsu, kuma an ga ɗaya yana tattara jakunkunan masu ibada da suka gudu.

Wasu mazauna yankin sun ce harin ya faru ne kusan ƙarfe 6 na yamma, kuma yankin na fama da hare-hare a ’yan kwanakin nan. ’Yan sa-kai sun yi yunkurin dakile harin.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, Adekimi Ojo, ya tabbatar da harin, yana mai cewa jami’an tsaro sun mayar da martani nan take, tare da tabbatar da mutuwar mutum ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here