Majalisar dattawa ta nemi a ɗauki sabbin sojoji dubu 100 

0
40

Majalisar dattawa ta nemi a gudanar da bincike kan fiye da dala miliyan 30 da aka kashe a shirin tsaron makarantu tun daga 2014 zuwa yau, bayan mummunan harin da aka kai wa makarantar ’yan mata ta Maga a jihar Kebbi.

Sanata mai wakiltar Kebbi ta arewa, Abdullahi Yahaya na Kebbi, ne ya gabatar da kudurin. Yan majalisar sun nuna ɓacin ransu kan yadda ’yan bindiga suka kashe mataimakin shugaban makarantar, suka jikkata wani ma’aikaci, sannan suka sace ɗalibai 25 duk da kasancewar jami’an tsaro a wurin.

Shugaban majalisa Godswill Akpabio, da ya jagoranci zaman, ya fara da minti ɗaya na shiru don tunawa da mamacin, tare da addu’a ga ’yan matan da aka sace.

Sanata Adams Oshiomhole ya soki shirin tsaron makarantu, yana mai cewa dukiyar da aka kashe bai kawo wani gagarumin sauyi ba. Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta dauki karin sojoji 100,000 domin karfafa rundunar tsaro.

Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki yadda aka kashe kudaden shirin tsaron makarantun, sannan ta amince da shawarar daukar matasa 100,000 zuwa aikin sojoji tare da siyan kayan aikin zamani wajen dakile matsalar tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here