Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja yau Laraba domin gudanar da ziyarar kwanaki biyu zuwa Johannesburg a Afirka ta Kudu da kuma Luanda dake Angola.
A sanarwar da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa ziyarar birnin Johannesburg ce matakin farko, inda Shugaban zai halarci taron shugabannin ƙasashe 20 masu ƙarfin tattalin arziki wato G20.
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ne ya gayyaci Tinubu, a matsayin sa na shugaban kungiyar G20.
Taron zai gudana tsakanin ranakun 22 zuwa 23 na watan Nuwamba, inda za’a tattauna kan batutuwa masu muhimmanci kamar tattalin arziki, rage bashin Æ™asashe, canjin yanayi, hanyoyin samar da makamashi masu dorewa, samar da abinci, ma’adanan duniya, da tasirin fasahar AI ga ci gaban bil’adama.


