Fitaccen ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya kai ziyara ga Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara a gidan yarin Kuje da ke Abuja.
BBC ta rawaito cewa, Sowore ya bayyana ziyarar ta shafin sa na Facebook, inda ya wallafa hotuna tare da rubuta cewa ya je tare da Barista Hamza Nuhu Dantani domin jajanta wa malamin da ke tsare.
A cewar sa, Sheikh Abduljabbar na ci gaba da fuskantar hukuncin kisa da aka yanke masa a Kano a zamanin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, kan zargin yin ɓatanci , zargi da Sowore ya danganta da siyasa.
Duk da haka, Sowore ya bayyana cewa sun tarar da Sheikh Abduljabbar cikin natsuwa, yana mai jaddada cewa Allah ne ke kula da shi, kuma zai ci gaba da tsayawa kan koyarwar da ya yi imani da ita.
Sowore ya jaddada cewa babu wanda ya kamata ya fuskanci zalunci ko rashin adalci, yana mai kira da a tabbatar da adalci ga Sheikh Abduljabbar, tare da kawo ƙarshen abin da ya kira amfani da addini wajen cimma muradin wasu ’yan siyasa.”


