ASUU tayi barazanar sake shiga yajin aiki a faɗin Najeriya

0
15

Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU reshen Kano ta zargi gwamnatin tarayya da jinkirta sake fasalin yarjejeniyar da ake tattaunawa a kai, tana mai cewa hakan na iya jefa jami’o’i cikin sabon yajin aiki idan wa’adin wata guda da aka bai wa gwamnati ya ƙare ba tare da aiwatar da alkwuran da aka ɗaukar wa ƙungiyar ba.

A sanarwar da ta fitar ranar 17 ga Nuwamba, kungiyar ta ce zaman majalisar zartarwar da aka yi a jihar Taraba ya nuna cewa gwamnati ba ta nuna cikakkiyar niyya wajen magance matsalolin ASUU ba, duk da dakatar da yajin aikin gargadi da ƙungiyar ta yi domin tattaunawa da gwamnati.

ASUU ta ce duk da an biya wasu tsoffin bashin ƙarin girman maaikata da wasu ƙananan kudade, gwamnati ba ta magance manyan matsalolin da suka shafi yanayin aiki da rayuwar malamai ba. Haka kuma ta yi Allah-wadai da kafa sabbin jami’o’i ba tare da isasshen tsarin kuɗi gudanarwa ba.

Kungiyar ta yi kira ga sarakuna, shugabannin addini, dalibai da sauran ’yan Najeriya su matsa wa gwamnati lamba domin ta cika alƙawurran da aka yi, domin guje wa sake rufe jami’o’i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here