Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya ɗaura aure da Hindatu Ada’u Isah, wacce take jami’a a Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF).
An gudanar da bikin ne a cikin ƙaramar liyafa a gidauniyar Madakin Rano, mahaifin amaryar, dake Ƙaramar Hukumar Rano ta Jihar Kano.
Hindatu ita ce ‘yar Alhaji Ada’u Isah, tsohon ɗan majalisa mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure. Manyan baki sun halarci taron, ciki har da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, shugaban kamfanin A.A Rano, da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Kano, Kabiru Alhassan Rurum, da wasu fitattun mutane.


