Masu aikin Umrah sun mutu a hanyar Madina zuwa Makkah

0
8

Alhazai Indiyawa 42 da ke kan aikin Umrah sun rasu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a daren Litinin, a kan hanyar Madina zuwa Makka.

Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare agogon Saudiyya, lokacin da wata motar safa mai ɗauke da mutane 43 ta yi karo da wata tankar man fetur.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum ɗaya kawai ne ya tsira daga cikin dukkan fasinjojin motar.

Ministan Harkokin Wajen Indiya, Dr. S. Jaishankar, ya bayyana a shafinsa na X cewa jakadancin kasar a Riyadh da Jeddah suna ba da cikakken taimako ga wadanda abin ya rutsa da su. Ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here