Matashi dan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya ji wa ‘yan uwansa rauni a Amurka

0
8

‘Yan sandan New Orleans, Amurka, sun kama Chukwuebuka Eweni, matashi dan Najeriya mai shekaru 27, bisa zargin kashe mahaifinsa da kuma jikata ‘yan uwansa biyu da wuka.

Iyalansa sun shaida wa jaridar WWL Louisiana cewa Chukwuebuka yana fama da wata matsalar lafiya ta kwakwalwa tun da dadewa, amma duk da haka baya nuna tashin hankali. Sun ce haka kawai ya dauki wuka ya caka wa mahaifinsa, Samuel Eweni, da ‘yan uwarsa biyu a cikin dare.

Samuel, wanda malami ne a fannin Computer Science a Southern University, ya rasu a wurin da lamarin ya faru. Daya daga cikin ‘yan uwansa ta samu sallama daga asibiti, yayin da ɗayar ke ci gaba da jinya amma tana cikin yanayi mai kyau.

Bayan faruwar lamarin, rahotanni sun nuna cewa Chukwuebuka ya garzaya New Orleans East Hospital domin neman taimakon lafiyar kwakwalwa, kamar yadda yake yawan yi. Ba tare da sanin abin da ya aikata ba, asibitin ya tura shi wata cibiyar jinya a Jefferson Parish. A can ne ‘yan sanda suka gano inda yake, suka kuma kama shi washegari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here