Hukumar tsaron al’umma ta farin kaya DSS ta kama wani da ake zargin shine babban mai kerawa da rarraba makamai, a jihar Filato, mai suna Musa Abubakar, a Mista Ali da ke ƙaramar hukumar Bass.
Rahotonni sun ce ya dade yana taka muhimmiyar rawa wajen samar da makamai ga kungiyoyin ta’addanci da ’yan bindiga a yankin arewa.
An kama shi ne a ranar 12 ga Nuwamba, 2025, bayan watanni ana sa ido tare da tattara sahihan bayanan sirri a kan sa. Rahotanni sun nuna cewa jami’an DSS sun same shi a lokacin da yake tsaka da haɗa abubuwan fashewa, inda aka tarar da kayayyaki da dama kamar sinadarai, na’urorin sarrafa ƙarfe, da bindigogi da ba a gama haɗawa ba.
A cewar DSS, Abubakar ya amsa cewa yana kerawa da kuma sayar da manyan makamai ga ƙungiyoyin da ke da hannu wajen hare-hare, garkuwa da mutane da rikice-rikice a Plateau da wasu jihohin arewa.
A wani rahoto daban, an sake kama Abdulazeez Obadaki, wani fitaccen ɗan kungiyar Ansaru da ya tsere lokacin karyewar kurkukun Kuje a 2022. Ana zargin Obadaki da kai hare-hare da dama, ciki har da fasa bankuna a Edo da kuma harbin wani dalibi a Okene.


