Tsohon Ministan Ayyuka na Musamman da Hulɗa tsakanin Jihohi, Kabiru Tanimu Turaki, ya zama sabon Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa a yayin taron gangamin jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan ranar Asabar.
Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin tsohon sanata mai wakiltar Anambra Central, Ben Obi, wanda ya bayyana cewa Turaki ya tsaya takara shi kaɗai bayan ɗan takarar Katsina a 2023, Lado Danmarke, ya janye kafin zaɓen. Duk da janyewarsa, Danmarke ya samu kuri’u 275 yayin da Turaki ya samu 1,516, daga cikin kuri’u 1,834 da aka kaɗa, 43 suka lalace.
Ben Obi ya kuma sanar da cewa Solarin Sunday Adekunle ya lashe kujerar Mataimakin Sakataren Shirye-shiryen Jam’iyya da kuri’u 633. Wasu kujeru biyu Shugaban Matasa da Mataimakin Lauyan Jam’iyya an dakatar da zaɓen su.
Gwamnonin da suka halarci taron sun haɗa da:
Bala Mohammed (Bauchi)
Seyi Makinde (Oyo)
Ahmadu Fintiri (Adamawa)
Dauda Lawal (Zamfara)
Caleb Mutfwang (Plateau)
Wasu ba su halarta ba, ciki har da Ademola Adeleke (Osun), Sim Fubara (Rivers), da Agbu Kefas (Taraba).


