PDP ta kori Wike, Fayose, Anyanwu da wasu jiga-jigai 8

0
8

Jam’iyyar PDP ta sanar da korar Nyesom Wike, Ministan Abuja; Ayo Fayose, tsohon Gwamnan Ekiti; da Samuel Anyanwu, wanda aka dakatar daga matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.

An bayyana hukuncin korar ne a ranar Asabar a lokacin babban taron gangamin PDP da aka gudanar a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Sauran da aka kori sun haɗa da:

Umar Bature, Ajibade Kamarudeen, Mao Ohabunwa, Uwachukwu, George Turner, Dan Orbih, Mohammed Abdulrahman, Austin Nwachukwu da Abraham Amah.

Olabode George, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (Kudu), ne ya gabatar da shawarar korar, sannan shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Buga, ya mara masa baya. Daga nan Gwamnan Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed, ya tura batun zuwa kuri’ar muryar mahalarta taron, sannan aka amince da hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here