Kwankwaso ya yi gargadi a kan rikicin sarautar Kano

0
11

Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce duk wanda yake kiran kansa a mat Sarkin Kano ban da Muhammadu Sanusi II, ba ya yi ƙarya.

Kwankwaso ya yi wannan ikirari ne yayin bikin yaye ɗalibai karo na huɗu na jami’ar Skyline, inda ya ce duk wani yunƙuri na kafar–ungulu wajen nada wasu sarakuna daga ko’ina, ba su dacewa ta doka ko karɓuwa a wajen al’umma.

Kwankwaso ya yaba wa jami’ar Skyline bisa naɗa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin uban jami’ar, yana mai cewa Sanusi ya daɗe yana jajircewa wajen inganta ilimi. Ya kuma jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here