Kano Na Fuskantar Barazana Tsaro – Kwankwaso

0
7

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Jihar Kano na fuskantar barazanar tsaro sakamakon ƙaruwa da yawaitar ‘yan bindiga da ke shigowa daga makwabtan jihohi.

Daily News 24 ta ruwaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin kammala karatun ɗalibai karo na huɗu na Jami’ar Skyline, inda ya yi gargadin cewa ‘yan bindiga daga Jihar Katsina na cigaba da addabar yankunan iyakar Kano.

Ya ce, “Kano ta kasance cikin kwanciyar hankali, amma a wannan lokacin wasu kananan hukumomi da ke kan iyakar Katsina kamar Shanono, Bagwai da Tsanyawa na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da ke shigowa daga Katsina.”

Kwankwaso ya bayyana cewa yan bindigar suna shigowa Kano ne su aikata laifuka sannan su koma cikin Katsina. 

Sai dai ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da jami’an tsaro bisa jajircewarsu da sadaukarwa, sannan ya jaddada cewa wajibi ne gwamnatin tarayya ta shiga tsakani don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.

A sakonsa ga ɗaliban da suka kammala karatu, Kwankwaso ya taya su murna tare da shawartar su da su rungumi tarbiyya mai kyau, kirkire-kirkire da kishin ƙasa a matakin rayuwar da za su shiga a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here