Rundunar sojin ƙasa ta musanta labarin sace babban jami’in ta a Borno

0
10

Sojojin Najeriya sun tabbatar da farmakin da ’yan ta’adda suka kai wa rundunar ko ta kwana ta 25 Task Force Brigade a jihar Borno, amma sun ƙaryata jita-jitar cewa an sace kwamandan rundunar.

A cikin wata sanarwa, Mataimakiyar Daraktar Yaɗa Labarai ta Rundunar Soja, Appolonia Anele, ta ce sojojin sun shiga cikin kwanton bauna ne yayin dawowa daga wani aikin sintiri a dajin Sambisa.

Ta tabbatar da cewa sojoji biyu da ’yan CJTF biyu sun rasa rayukansu a harin.

Anele ta ce kwamandan rundunar, Brigadier General M. Uba, wanda ya jagoranci aikin, ya jagoranci tawagar da ƙarfin guiwa har suka fatattaki ’yan ta’addan.

Ta kuma bayyana cewa rahotannin da ake yadawa cewa an yi garkuwa da kwamandan, ba gaskiya ba ne, don haka ta bukaci jama’a su yi watsi da labarin.

Rahotonni sun ce waɗanda suka mutu daga CJTF an kai su Maiduguri domin jana’iza.

Babban Hafsan Sojan ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya yaba da jarumtar sojojin tare da jajanta wa iyalan mamatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here