Libya ta koro ‘yan Najeriya 80 saboda wasu dalilai 

0
14

Hukumar kula da baƙin haure ta kasar Libya ta sanar da cewa ta kori wasu ‘yan Najeriya 80 da aka tsare a wasu cibiyoyi da ke fadin ƙasar saboda rashin takardun zama a ƙasar. Wannan mataki na cikin ƙoƙarin gwamnati na rage cunkoson da ake fama da shi a wuraren tsare baƙin haure marasa izinin zama.

An aiwatar da korar ne a ranar Laraba daga filin jirgin sama na Mitiga da ke birnin Tripoli.

Rahotanni sun nuna cewa wannan kora tana daga cikin shirin da Libya ke gudanarwa don rage yawan baki marasa izini da ke cikin kasar, musamman a cibiyoyin tsare mutane da ake fama da cunkoso da rashin kyawun yanayi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here