Abubuwan da ya kamata ku sani game da mamallakin filin da Wike ya yi takaddama a kansa

0
8

Abubuwan da ya kamata ku sani dangane da mamallakin filin da Wike ya yi takaddama a kansa

An samu tashin hankali a wani filin da ake takaddama a kan ss a unguwar Gaduwa, dake Abuja, bayan da Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi arangama da wasu jami’an soja.

Wike ya ziyarci filin da ke kan lamba 1946, Buffer Transit, Southern Parkway, domin duba yadda wasu jami’an Rundunar Sojan Ruwa suka hana ma’aikatan kula da ci gaban birnin gudanar da aikinsu. Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun zo wurin ne bisa umarnin wani tsohon babban jami’in soja mai murabus.

A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga Wike yana muhawara mai zafi da wani jami’in soja mai suna AM Yerima. Wannan lamari ya haifar da cece-kuce kan dangantaka tsakanin farar hula da jami’an tsaro a ƙasar nan.

Da yake magana da manema labarai, Wike ya ce mamallakin filin wanda aka gano tsohon shugaban rundunar sojan ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo, ne bai gabatar da takardun mallaka ko izinin gina wajen ba.

> “Ba zan lamunci barazana daga kowa ba, ko da tsohon jami’in soja ne. Ya kamata ya zo ofishina da takardunsa idan yana da gaskiya,” in ji Wike.

Rahotonni sun ce Gambo ya sayi filin tun a shekarar 2020.

Wanene Awwal Gambo ?

Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo, wanda aka haifa a Ƙaramar hukumar Nasarawa Kano a ranar 22 ga Afrilu, 1966, ya yi karatu Firamare a makarantar Gwagwarwa, sannan ya wuce Rumfa College kafin ya shiga makarantar horar da sojoji (Nigerian Defence Academy) a 1984. Ya ƙware a harkar leƙen asiri da yaƙin ruwa a ƙasan teku, kuma ya halarci manyan kwasa-kwasai na soja a Najeriya da Afirka ta Kudu.

Ya riƙe manyan mukamai a Rundunar Sojan Ruwa kafin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi shugaban rundunar a Janairu 2021. A lokacin shugabancin, Gambo ya yi fice wajen yaƙi da satar man fetur.

An sauke shi daga mukamin a watan Yuni 2023, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here