Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan Najeriya, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya ce bidiyoyin da suka bayyana a kafafen sada zumunta yana yin walwala da ƙwambo a Landan, saƙo ne ga abokan hamayyarsa na siyasa.
A wata hira da BBC, Doguwa ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin nuna wa maƙiyansa daga Doguwa da Tudun Wada cewa har yanzu shi ne wakilinsu, duk da ƙiyayya da suka nuna masa.
Ya ce: “Na yi waɗannan hotuna ne a matsayin barkwanci da aikawa da saƙo ga maƙiya cewa ni dai Doguwa ne, kuma na tsira.”
Doguwa ya ƙara da cewa iyalinsa sun san halinsa na barkwanci, don haka ba su ɗauki abin da muhimmanci ba. Ya kuma bayyana cewa siyasa ana yin ta ne bisa yanayin mutanen yankin da kake wakilta, kuma ina da damar yin magana da Turanci idan bukata ta taso.


