Shugaba Bola Tinubu ya tura ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar, da ministan shari’a, Lateef Fagbemi, zuwa Burtaniya domin tattauna yiwuwar a dawo da Ike Ekweremadu Najeriya ya ci gaba da zaman gidan yari.
Tawagar ta gana da ma’aikatar shari’a ta Burtaniya, inda suka nemi a ba da damar mayar da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan, wanda aka yanke wa hukuncin sama da shekaru 9 a 2023 kan laifin safarar sassan jiki.
An kama Ekweremadu da matarsa tun a shekarar 2022 kan shirin dasa ƙoda ga ’yarsu ba bisa ka’ida ba, ta hanyar yiwa wani yaro rufa-rufar cire kodar sa domin sanyaya yar Ekweremadu, zuwa yanzu Matarsa ta kammala zaman hukuncin ta a Burtaniya ta dawo Najeriya tun cikin wannan shekara.


