Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa tana shirin daukar karin ma’aikatan lafiya kimanin 9,000 a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya sanar da haka a Kaduna yayin wani taron yini guda da aka shirya domin tattaunawa da kafafen yada labarai. Taron na cikin wani shiri da Hukumar Inshorar Lafiya ta Kaduna (KADCHMA) ta shirya tare da hadin gwiwar kungiyar lafiya ta Lafiya ta haɗin gwiwar Najeriya da Burtaniya.
Maiyaki ya ce Gwamna Uba Sani ya riga ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 1,800 nan take a fannoni daban-daban, kuma za a ci gaba da wannan tsarin a duk tsawon shekara biyar da ke tafe domin karfafa bangaren kiwon lafiya a jihar.
Ya ce gwamnan ya sanya kiwon lafiya cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ke bai wa muhimmanci.


