Akwai buƙatar jami’o’i masu zaman kansu su shiga ƙungiyar ASUU–NLC

0
12

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya bukaci a haɗa jami’o’in Najeriya masu zaman kansu a  cikin ƙungiyar malaman jami’a, ASUU. Ya ce lokaci ya yi da ASUU za ta fara tattaunawa da shugabannin waɗannan jami’o’i domin su fahimci muhimmancin yin aiki tare don kare muradun ilimi.

Ajaero, wanda ya yi wannan bayani a wata tattaunawa da shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna, a shirin Toyin Falola, ya jaddada cewa ya kamata a daina cin zarafin mambobin ASUU. Ya kuma nuna mamaki kan yadda gwamnati ta gaza cika yarjejeniyar da ta kulla da ASUU tun shekarar 2009.

Ya bayyana cewa an ƙirƙiribASUU ne don a raba ta da NLC, sannan gwamnati ta hana ASUU zama a ƙarƙashin NLC, abin da suka garzaya kotu suka yi nasara a kai. Ajaero ya ƙara da cewa dalilin kafa jami’o’i masu zaman kansu shi ne rage ƙarfin ASUU, don haka dole a tabbatar da cewa su ma sun shiga ƙungiyar domin karfafa muradun malamai gaba ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here