Gwamnatin tarayya ta ce alkaluman da ta tattara sun nuna cewa ana samun nasarar shawo kan matsalar tsaron da ta addabi sassan Nigeria da sama da kashi 80 cikin dari.
Wannan na zuwa yayin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargadi ga ‘yan kasar ta da su kaurace wa yin balaguro zuwa wasu sassan Najeriya bayan nuna damuwa kan karuwar hare-haren ta’addanci da satar mutane.
Jihohin da gwamnatin Birtaniya ta yi gargadin sun hada da Borno da Yobe Katsina da Zamfara da Adamawa da Gombe da kuma wasu jihohin na kudanci.
Sai dai gwamnatin tarayya ta ce alkaluman ta na shekarar 2025 sun nuna ana samun saukin hare-haren da ake kai wa da satar jama’a.
Gwamnatin ta ƙara da cewa daga shekarar 2024 zuwa yanzu, ta samu nasarar gabatar da ƴan ta’adda da ƴan bindiga sama 124 a kotu da aka yanke wa hukunci, sannan ta ce akwai wasu kamar jagororin Ansaru da waɗanda suka kai hari a asibitin Owo a 2022 da na Yelwata da sauransu da suke fuskantar shari’a.


