Ɗan majalisa mai wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC mai mulki, bayan ficewa daga jam’iyyar NNPP.
Matakin ya zo ne bayan watanni biyu da NNPP ta kore shi, inda jam’iyyar ta zarge shi da aikata abubuwan da suka saba wa dokoki da manufofinta, tare da gazawa wajen biyan kuɗin jam’iyya.


