Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da cewa an sako Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Muhammad Samaila Bagudo, wanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi kwanakin baya.
Majiyar majalisar ta shaida wa BBC cewa Bagudo ya dawo gida cikin koshin lafiya bayan wasu kwanaki a hannun masu garkuwa.
Har yanzu ba a tabbatar ko an biya kudin fansa ba, amma majiyar ta ce majalisar ta gode wa duk masu ruwa da tsaki da suka yi aiki tare domin ganin an kubutar da shi.
An sace shi ne a ranar 31 ga Oktoba, kusa da gidansa da ke garin Bagudo.


