Gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da masu lalata hanyar Abuja zuwa Kano

0
15

Ƙaramin ministan ayyuka, Bello Goronyo, ya nuna damuwa kan ɓarnar da wasu mutane ke yi ga aikin babbar hanyar Abuja–Kaduna zuwa Kano.

Yayin duba aikin a ranar Asabar, Goronyo ya ce an samu matsalolin da suka haɗa da fasa sassan hanya da sace ƙarafa, lamarin da ke haifar da asara a aikin.

Ya ce aikin na tafiya sosai, kuma hanyar tana kara yin kyau, amma ana bukatar mutanen da ke kusa da hanyar su dakatar da lalata hanyoyi don tabbatar da dorewar nasarar aikin.

Goronyo ya jaddada cewa kula da hanya na taimakawa tsaro, rage haɗurra, da inganta zirga-zirga. Ya bayyana cewa tun bayan fara aikin, matsalolin tsaro a hanyar Abuja ta ragu.

A nasa bangaren, Daraktan Hanyoyi na Tarayya, Clement Ogbuagu, ya ce aikin yana tafiya da sauri kuma ingancinsa ya gamsar da su. Ya tabbatar cewa ma’aikatar ba za ta yi wasa da wannan muhimmin aiki ba, domin yana daga cikin manyan hanyoyin da gwamnatin tarayya ke yin alfahari da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here