Soludo ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Anambra
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da Farfesa Chukwuma Charles Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya sake lashe zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar Anambra ranar Asabar.
Soludo, wanda ya nemi wa’adi na biyu, ya yi takara ne tare da sauran ‘yan takara 15 da suka haɗa da Prince Nicholas Ukachukwu na APC, Paul Chukwuma na YPP, John Nwosu na ADC da George Moghalu na LP, da sauran su.
Da yake bayyana sakamakon ƙarshe, jami’in tattara sakamakon jihar, Farfesa Edoba B. Omoregie (SAN) ya bayyana cewa:
Jimillar masu kada kuri’a a jihar: 2,788,864
Adadin da suka fita aka tantance: 598,229
Kuri’un da suka inganta: 584,054
Kuri’un da aka ƙi karɓa: 11,244
Jimillar kuri’un da aka kada: 595,298
A sakamakon ƙuri’un da ‘yan takara suka samu:
APGA (Soludo): 422,664
APC (Ukachukwu): 99,445
YPP (Paul Chukwuma): 37,753
LP (Moghalu): 10,576
ADC (Nwosu): 8,208
Ya ƙara da cewa:
“Ni ne jami’in bayyana sakamakon wannan zaɓe. Ina tabbatar da cewa Farfesa. Charles Chukwuma Soludo ya samu nasara kuma an sake zaɓensa a matsayin Gwamnan Anambra.”


