Mazauna Dangoro a Kumbotso, Jihar Kano, sun yi addu’o’in neman taimakon Allah kan abin da suka kira ci gaba da kwace musu gonaki da filaye da gwamnati ke yi.
Addu’ar ta biyo bayan rahoton cewa gwamnati na shirin mayar da kasuwar ’Yan Lemo da ta Yankaba zuwa yankin, lamarin da mazauna ke ganin zai kara jefa su cikin matsalar rasa matsuguni.
Wani da abin ya shafa, Sadiq Muhammad Abdullahi, ya ce wannan shi ne karo na huɗu da irin haka ke faruwa a Dangoro. Ya bayyana cewa daga cikin filaye takwas da yake da su, gwamnati ta bar masa fili ɗaya da rabi kawai.
Wani mazaunin yankin, Comrade Nuraini Adabayo, ya ce lamarin ya jefa al’umma cikin rudani, musamman ganin cewa mutane da dama sun riga sun sayi filaye bisa kwarin gwiwar cewa gwamnatin ba za ta sake auna yankin ba. Yanzu sama da filaye 40 ne abin zai shafa.
Wani jigo a yankin, Alhaji Gambo Saminu Adamu, ya bukaci gwamnan ya ziyarci Dangoro don ganin halin da ake ciki.
Mazaunan sun sha alwashin ci gaba da addu’a tare da roƙon gwamnati ta dakatar da shirin, saboda yana barazana ga rayuwarsu.


