Gwamnatin Kano zata ɗauki mataki akan kamfanonin sadarwa da bankuna, akan allon talla

0
9
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Hukumar Kula da Tallace-tallace da Alluna ta Jihar Kano (KASA) ta bawa bankuna da kamfanonin sadarwa wa’adin mako guda su cire allunan tallan da aka kafa ba tare da bin ka’ida ba, kamar yadda kotu ta umarta.

Darakta-Janar na KASA, Kabir Dakata, ya ce hukumar ta raba takardun umarnin kotu ga duk cibiyoyin da abin ya shafa. Ya bayyana cewa an dauki matakin ne saboda kamfanonin sun ki bin dokokin da ke tsara kafa allunan talla a jihar.

Ya ce kotu ta umarci kamfanonin su cire tallan da kansu, kuma idan suka kasa yin hakan, hukumar za ta cire su sannan za a dorawa kamfanonin kudin cirewar, bisa doka.

Dakata ya kara da cewa an ba su wa’adin mako guda kafin daukar mataki na gaba, domin tabbatar da adalci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here