Ba za’a gudanar da zaɓen gwamna a wasu yankunan jihar Anambra ba–INEC

0
13

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta fara rarraba muhimman kayan zaɓe zuwa ga ƙananan hukumomi daban-daban na Jihar Anambra, domin shirye-shiryen zaɓen gwamna da za a yi a ranar Asabar.

An fara rarrabawar ne a ofishin INEC na Awka a ranar Alhamis, ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

Kwamishinan Zaɓe Reshen Jihar, Queen Agwu, tare da Kwamishinan ’Yan Sanda da ke kula da tsaro a lokacin zaɓe, Abayomi Shogunle, sun jagoranci aikin. Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa jami’anta sun gama shiri don kare yankunan ƙasa da na ruwa yayin zaɓen.

INEC ta tabbatar da cewa masu ƙuri’a 2,802,790 ne za su kada ƙuri’a a rumfunan zaɓe 5,718 da ke cikin ƙananan hukumomi 21 na jihar. Haka kuma, hukumar ta ce ba za a gudanar da zaɓe a rumfuna biyu ba, saboda babu masu rajista a can.

Zaɓen na bana ya ƙunshi ’yan takara 16, ciki har da:

Chukwuma Soludo (APGA)

Nicholas Ukachukwu (APC)

Paul Chukwuma (YPP)

George Moghalu (LP)

Jude Ezenwafor (PDP)

Da sauran ’yan takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here