Shugaban ƙungiyar IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu, ya aika wa Shugaban Amurka Donald Trump da wasiƙa yana neman gudanar da bincike kan abin da ya kira hare-haren da ake kai wa Kiristoci da al’ummar Igbo a yankin Kudu maso Gabas.
Wasiƙar, wadda lauyansa Aloy Ejimakor ya miƙa wa Ofishin Jakadancin Amurka a Abuja a ranar 6 ga Nuwamba 2025, ta yi nuni da sanarwar Trump ta kwanan nan cewa Amurka na iya dakatar da tallafi ko ma yin shirin tsoma baki idan gwamnatin Najeriya ta gaza kare Kiristoci.
Kanu ya roƙi Amurka ta jagoranci cikakken bincike da damar shiga wuraren faruwar al’amura, shaida daga wadanda suka tsira, da kuma binciken kaburburan da aka binne mutanen da aka kashe. Ya ce Kiristoci a yankin Igbo na fuskantar barazana mai tsanani.


