Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayar da umarni ga rundunar sojin ƙasar da ta tanadi tsare-tsaren yiwuwar shiga cikin Najeriya, bayan ya sake jaddada zargin cewa ana kashe Kiristoci da yawa a ƙasar.
A wani bidiyo da Fadar White House ta wallafa a ranar Laraba, Trump ya bayyana lamarin a matsayin “barazana ga wanzuwar addinin Kirista,” yana zargin “’yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi” da kisan gilla.
Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya tabbatar da umarnin, inda ya umurci rundunar AFRICOM da ke Jamus ta gabatar da jadawalin shiga cikin Najeriya guda uku, mai sauƙi, matsakaici da kuma mai ƙarfi.
Zaɓin mai sauƙi zai haɗa da taimaka wa dakarun Najeriya ta hanyar musayar bayanan sirri da goyon bayan aiki kaɗan.
Zaɓin matsakaici zai ba da damar kai harin jiragen sama marasa matuƙa (drone) kan sansanonin ‘yan ta’adda.
Zaɓin mai ƙarfi kuma ya haɗa da tura jirgin ruwa mai ɗaukar jiragen sama zuwa Tekun Guinea don kai hare-hare daga sama, duk da cewa jami’ai sun ce hakan ba zai yiwu ba saboda wasu manyan ayyukan duniya.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa tana maraba da duk wani taimako daga Amurka wajen yaƙi da ta’addanci, amma ta jaddada cewa dole ne a mutunta ikon ƙasar.


