Zanga-zanga ta janyo rufe majalisar wakilai tsawon kwanaki 7

0
12

Majalisar wakilai ta dakatar da zaman ta na tsawon mako guda bayan wata zanga-zangar da ƙananan ‘yan kwangila suka yi a majalisar dokoki ta ƙasa.

Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talata.

Dalilin Zanga-zangar

A safiyar Talata, ƙungiyar ‘yan kwangila na cikin gida suka mamaye harabar majalisar suna neman a biya su kudin ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024. 

Rahotonni sun ce ‘yan kwangilar sun dade suna zanga-zanga a ma’aikatun gwamnati daban-daban, ciki har da ma’aikatar kuɗi da ta ayyuka. Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ya ce an yi taro da su sau da dama don warware matsalar, kuma ministan kuɗi, Wale Edun, ya yi alkawarin biyan  hakkokinsu, amma har yanzu ba a aiwatar da hakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here