Fitaccen mawaƙin Nijeriya da ke zaune a Amurka, Damini Ogulu wanda aka fi sani da Burna Boy, ya bayyana cewa ya karɓi addinin Musulunci.
A cewar mai amfani da kafar sada zumunta Very Dark Man, wanda ya tabbatar da labarin a shafin sa na X, mawaƙin ya canza sunansa zuwa Abdulkareem bayan ya shiga Musulunci.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa Burna Boy ya dauki wannan mataki ne bayan dogon bincike da neman fahimtar gaskiya game da Ubangiji.
Rahotanni sun ce tun bayan musuluntarsa, mawaƙin ya bayyana cewa addu’o’insa suna samun karɓuwa daga Allah cikin sauƙi.


