Barazanar Trump ta haifar da fargabar tattalin arziki ga Najeriya–CPPE

0
13

Maganar da  shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi cewa zai iya tura sojojinsa zuwa Najeriya domin yaƙi da “masu kashe kiristoci”, ta tayar da hankula a cikin gida da wajen ƙasa, inda masana tattalin arziki da jami’an gwamnati suka yi martani mai ƙarfi.

Cibiyar Bunkasa Kasuwanci da Zuba Jari (CPPE) ta gargadi cewa barazanar na iya janyo ficewar masu zuba jari daga Najeriya.

Dr. Muda Yusuf, shugaban CPPE, ya ce irin wannan magana daga shugaba mai tasiri a duniya na iya lalata martabar Najeriya da tsoratar da masu zuba jari.

> “Ko da barazana ce kawai, ta riga ta shafi amincewar masu saka jari,” in ji Yusuf.

Cibiyar ta yi gargadin cewa wannan na iya haifar da faduwar darajar hannun jari, hauhawar bashi, da raunin Naira. Ta ba da shawarar a hanzarta tattaunawar diflomasiyya da Amurka don rage tashin hankali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here