Matasa sun farmaki tawagar gwamnan jihar Neja

0
10

Jam’iyyun adawa da dimbin masu kada ƙuri’a a Jihar Neja sun nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar, suna zargin hukumar zaɓe ta NSIEC da yin maguɗi tare da jam’iyyar APC mai mulki.

Rahotanni daga ƙananan hukumomi 25 na jihar sun nuna jinkiri ko ma rashin isowar kayan zaɓe gaba ɗaya a wasu rumfunan zaɓe. Wasu sun yi zargin cewa an shirya tsarin ne domin hana mutane kada ƙuri’a da kuma cusa sakamakon ƙarya.

Duk da cewa hukumar ba ta fitar da cikakken sakamako ba, APC na kan gaba sosai a yawancin kujeru, abin da ya haifar da tarzoma a wurare da dama ciki har da Suleja, Wushishi da Lavun, inda aka zargi jami’an tsaro da tsoratar da masu kada ƙuri’a.

Shugaban jam’iyyar SDP na Chanchaga, Hon. Isah Barau, ya bayyana zaɓen a matsayin wanda aka yi ba a tsarin gaskiya ba. Haka kuma jami’an PDP sun zargi ‘yan sanda da tsare musu jami’ai da kwace motocin jam’iyya.

Gwamnan jihar, Umar Bago, shi ma ya gamu da fushin matasa a garinsu na Bida, inda aka jefa duwatsu kan motocinsa har wasu suka jikkata. 

Rahotonni sun ce hakan ya faru sakamakon wani rabon kuɗi da aka yi wanda ya janyo hargitsi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here