Burna Boy ya bayyana dalilin sa na komawa addinin musulunci

0
11

Fitaccen mawakin Najeriya mai lambar yabo ta Grammy, Burna Boy, ya bayyana cewa dalilin da yasa ya musulunta daga Kiristanci shi ne bincike da neman gaskiya da natsuwa ta hanyar addini.

A wata tattaunawa da ya yi da mai shirya shirin Playboymax, mawakin “African Giant” ya ce ya shiga bincike ne don fahimtar ma’anar rayuwa.

Burna Boy ya bayyana cewa bincikensa ya kai shi ga nazarin addinai daban-daban, inda kowanne ya koya masa darussa amma bai samu cikakkiyar amsa ba. “Yayin da nake ƙara bincike, haka nake ƙara rikicewa,” in ji shi, yana mai cewa tafiyarsa ta neman gaskiya tana ci gaba.

Ya ce musulunta ba yana nufin ya watsar da abin da ya yi imani da shi a baya ba, sai dai neman salama da daidaito da kuma kusanci da Ubangiji. Duk da haka, ya bayyana cewa bai kai cikakkiyar nutsuwa da yake nema ba tukuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here