Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga yankin Kogi ta Tsakiya ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da bayar da umarni ga shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS) a kan ƙwace mata fasfo a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
A cikin wani bidiyo da ta wallafa a yanar gizo, Natasha ta bayyana cewa wannan umarni ne ya hana ta tafiya ƙasashen waje.
Cikin fushi sanatar ta bayyana cewa kamar yadda aka yi mata makamancin haka a baya, a yanzu ma an ƙwace fasfo ɗin ta duk da cewa bata aikata laifin komai ba, tana mai cewa shugaban majalisar dattawa ne ke da alhakin wannan musgunawa da ta fuskanta.


